Matthew 6

Bayarwa ga Mabukata

1“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukan adalcinku’ a gaban mutane, domin su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.

2“Saboda haka saʼad da kake ba wa masu bukata, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majamiʼu da kuma kan tituna, don mutane su ba su girma. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun karɓi ladarsu cikakke. 3Amma saʼad da kake ba wa masu bukata, kada ka yarda hannun hagunka yǎ ma san abin da hannun damarka yake yi, 4don bayarwarka ta zama a ɓoye. Saʼan nan Ubanka mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

Adduʼa

5“Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin adduʼa a tsaye a cikin majamiʼu da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun karɓi ladarsu cikakke. 6Amma saʼad da kake adduʼa, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi adduʼa ga Ubanka wanda ba a gani. Saʼan nan, Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. 7Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu. 8Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.

9“To fa, ga yadda ya kamata ku yi adduʼa:

“ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,
a tsarkake sunanka,
10mulkinka yǎ zo
a aikata nufinka
a duniya kamar yadda ake yi a sama.
11Ka ba mu yau abincin yininmu.
12Ka gafarta mana laifofinmu,
kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.
13Kada ka kai mu cikin jaraba,
amma ka cece mu daga mugun nan.
Ko kuwa daga mugu; waɗansu rubuce rubucen hannun da ba su jima ba ɗaya, gama mulki da iko da ɗaukaka naka ne har abada. Amin.

14Gama in kuna yafe wa mutane saʼad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

Azumi

16“Saʼad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 17Amma saʼad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka, 18domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai ga Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

Ajiya a Sama

19“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan yi fashi, su yi sata. 20Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su yi fashi, su yi sata. 21Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za ta kasance.

22“Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. 23Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!

24“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yǎ ƙi ɗaya, yǎ ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yǎ yi aminci ga ɗaya, saʼan nan yǎ rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah ku kuma bauta wa Kuɗi gaba ɗaya.”

Kada Ku Damu

25“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?

26“Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko saʼa ɗaya
Ko kuwa kamu guda ga tsayinsa
?

28“Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33Sai dai da farko, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34Saboda haka kada ku damu game da gobe, domin gobe zai damu da kansa. Kowace rana tana da isashiyar damuwarta.

Copyright information for HauSRK